Labarai

Zulum da Pantami sun lashe lambar yabo ta Gwarazan Musulmai a fadin Najeriya cikin 2019

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umarar Zulum, ya samu lambar yabon Musulmi mafi kokari a Najeriya na shekarar 2019, na jaridar Musulmai, Muslim News, jaridar Musulunci ta daya a Najeriya.

Rahoton da Dabo FM ta samu daga jaridar LegitNg ya bayyana samun lambar yabon Farfesa Zulum bai zo da mamaki ba bisa ga irin bajintar da ya nuna a faggen shugabanci tun lokacin da aka rantsar da shi a watan Mayun 2019.

Duk da kasancewar jihar Borno cikin yaki da Boko Haram, Farfesa Zulum bai yi kasa a gwiwa wajen ganin cewa al’ummarsa sun debi romon demokradiyya ba.

A cewar jaridar, Zulum ya taka rawar gani a bangarori daban-daban irinsu tsaro, ilimi, kiwon lafiya, sufuri, tattalin arziki, da tallafi ga yan sansanin gudun hijra.

Gabanin zama gwamna, Farfesa Zulum ya kasance kwamishanan gine-ginen gidajen da Boko Haram suka lalata karkashin tsohon gwamna, Kashim Shettima.

Ga jerin wadanda suka samu lambar yabon:

1. Farfesa Babagana Umarar Zulum

2. Sheikh Dakta Isa Ibrahim Ali Pantami (Ministan sadarwa kuma tsohon shugaban hukumar NITDA)

Karin Labarai

Masu Alaka

Ko shugaban karamar hukuma na samu, zanyi -Isa Yuguda

Dabo Online

A najeriya, an haifi Jarirai sama da 26,000 a daren sabuwar shekarar – UNICEF

Dabo Online

Duk shifcin-gizo gwamnoni keyi a batun biyan Sabon Albashi -Kungiyar Kwadago

Muhammad Isma’il Makama

Ginin babban dakin karatun Abuja zai lakume Naira biliyan 50 – Ministan Ilimi

Dabo Online

Gwamnan Borno ya baiwa tsofaffin Ma’aikata 10,319 kudadensu na Fansho

Dabo Online

Kwastam ta fara raba shinkafa buhu 67,000

Dabo Online
UA-131299779-2