Abin Sha’awa: Dan kwallon Liverpool Sadio Mane ya shiga an wanke bandakin Masallaci tare dashi

Faifai bidiyon dan wasan kwallan kafar Liverpool kuma zakaran dan kwallon kafar duniya a matsayi na 4, kana gwarzon dan wasa na farko da yafi iya kwallon kafa a nahiyar Afirika, Sadio Mane ya karade shafukan sada zumunta.

Rahoton Dabo FM ya bayyana shahararren dan kwallon kasar Senegal din ya bayyana cikin faifan bidiyon yana zuba ruwa a cikin bokiti kana wani karamin yaro yana taya shi wanke kasan bandakin masallacin.

Majiyar mu ta tabbatar da cewa masallacin shine wanda dan kwallaon ke halarta a kowane lokacin sallah, wanda keda suna Masallacin Al Rahman dake kan titin Mulgrave, cikin birnin Liverpool ta kasar Birtaniya.

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.