//

Baturiya yar Amurka ta yo tsuntsun soyayya zuwa Kano don iske saurayinta dan Najeriya

0

Wata baturiya yar asalin birnin California na kasar Amurka, tayo tattaki har zuwa jihar Kano domin iske masoyinta dake a unguwar Panshekara ta birnin Kano.

DABO FM ta tattara cewar baturiyar mai suna Janet da saurayin nata mai suna Sulaiman sun hadu ne a dandalin sada zumunta na Facebook.

Janet ta bayyana cewar irin kalaman soyayya da Sulaiman yake yi mata ne yasa ta kasa jurewa har sai tazo tayi ido hudu da annurin zuciyar tata, kamar yacce ta bayyana a shirin Inda Ranka na gidan Rediyon Freedom na jihar Kano.

Alakar matashi Sulaimanu mai shekaru 23 da Madam Janet mai shekaru 43 tayi karfin da dukkaninsu suka amince wajen auren juna, har ma ta kara da cewa zata tafi dashi chan kasarsu ta Amurka.

Masu Alaƙa  Soyayya ta sanya Sa'id Muhammad ginawa matarsa gida mai kirar jirgin sama a Abuja

Shima a nashi bangaren, matashi Sulaimanu ya amsa bukatar auren wanda har ma iyayenshi sun amince da hakan, kamar yadda mahaifiyarshi, Haj Fatima Sulaiman ta bayyana.

Karin Labarai

Share.

About Author

Comments are closed.

%d bloggers like this:
©Dabo FM 2020