Labarai

Gazawar Gwamnati ce karara yin sulhu da ‘yan ta’adda-Shehu Aljan

Shahararren mai kama barayin nan, kuma shugaban kamfanin samar da tsaro ta Aljan Network Security Services of Nigeria Alhaji Shehu Musa Aljan, ya bayyana matakin da wasu gwamnoni ko shuwagabannin kananan hukumomi ke dauka na yin sulhu da ‘yan ta’adda a matsayin gazawa da bada kai bori ya hau daga bangaren gwamnati.

Ya bayyana haka ne a zantawarsa da Dabo FM, kwanaki kadan bayan gagarumar nasarar da ya samu na kwato daruruwan shanaye da barayi suka sace a karamar hukumar Giwan Jihar Kaduna.

Ya ce, a lokuta da dama koda an yi sulhun da su, ba su cika bayyana ainihin makaman da suka mallaka ba, ta yadda za’a gamsu cewa da gaske su ke suna bukatar sulhun kuma a zauna lafiya.

Ya kara da cewa, akwai bukatar wayarwa mutane kai game da wasu al’amura da suka shafi harkar tsaro a kasar nan, ta yadda kowwa zai bada nasa gudunmuwar domin kaiwa ga tudun mun tsira.

Da ya juya ga lamarin da ke faruwa a babban hanyar Kaduna zuwa Zariya da Kaduna zuwa Abuja kuwa, ya shawarci gwamnatin Jihar Kaduna ta kira masa ruwa da tsaki a harkar samar da tsaro, domin zuwa a hadu a hada karfi da karfe ta yadda za’a samu hanyar warware matsalar cikin sauki mai-makon a bari rayukan mutane na salwanta ba ji ba gani.

Sai dai ya yabawa sabon kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kaduna, wanda ya ce a sanin sa, mutum ne da yake jajirtacce kuma masanin dabarun magance kowanni rikici.

Shehu Aljan, ya ce, bayan daukar tsawon lokaci yana zagawa sassan kasar nan domin yaki da miyagun mutane, yanzu lokaci ya yi, da zai dawo jihar sa ta haihuwa, wato jihar Kaduna domin taimakawa kokarin gwamnati, matukar a shirye take na kawar da ayyukan barayin shanu da masu garkuwa da mutane domin naiman kudin fansa.

Ya bada misali ga irin nasarar da suka samu a karamar hukumar Giwa, inda suka gano shanaye masu dumbin yawa, da bindgogi har ma da albarusai, kuma daga karshe suka gano mamallakin su, suka damka shi ga hukuma.

Daga karshe ya yi fatan hukumta duk wanda suke kamawa kuma suna damka shi ga hukuma, saboda hakan ya zamto izina ga masu shirin aikata makamancin laifin.

UA-131299779-2