Labarai

Bauchi: Saurayi ya caccakawa budurwarshi wuka a gadon baya har lahira

Wani saurayi da aka bayyana da sunan Soloman Peters ya caccakawa budurwarshi wuka da tayi sanadiyyar barinta duniya.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya, NAN ya rawaito cewar Soloman ya cakawa budurwar tashi mai sunan Patience Zakari wuka sakamakon ta dauki kiran da wani saurayi yayi mata a ranar Juma’ar da ta gabata.

NAN ta rawaito cewar al’amarin ya faru ne da misali karfe 1:03 na daren Juma’a a gidan su mamaciyar dake unguwar Gwallameji a cikin garin Bauchi.

Wani makusancin masoyan da ya bukaci a sakaya sunanshi ya bayyana yadda mamaciyar, Patience Zakari ta bada lamarin abinda yasa suka samu sa-in-sa tsakaninsu da saurayin nata.

Ya bayyana cewar saurayin da ake zargi da kashe budurwar tashi da ita budurwar sun samu sa-in-sa mai zafi tsakaninsu biyo bayan amsa kiran waya da tayi a tsakar dare da wani saurayi.

“Ta fadamin duk abinda ya faru kafin mutuwarta wacce da faru da tsakar daren Juma’a.”

“Tace ta amsa kiran wani abokinta na mijin ne a tal-talen dare wanda hakan yasa saurayin nata Solomon ya fara kishi wanda har ya kai ya fara kyararta da munanan kalamai. Ko da tayi yunkurin yi masa bayani, sai dirar mata ya fara dukan ta.”

“Ta buga masa kwalba a kanshi don ta kare kanta domin dukan da yake mata yayi yawa, daga nan ya dauko wuka ya caka mata a baya.”

“Tace ta zubar da jini sosai kafin a kaita asibiti da safe wanda har aka bata kulawa ta dawo gida, shine take bani labari a yamma.”

“Kwatsam bayan tafiya ta, naji ance dinkin da akayi mata ya farke har an koma da ita asibiti inda a nan ne tace ga garinku nan.”

A nata bangaren, rundunar yan sandan jihar ta hannun kakakinta, DSP Kamal Abubakar, ta tabbatar da faruwar al’amarin tare da tabbatar da kama wanda ake zargi da mai asibitin da aka kai mamaciyar.

“Eh tabbas al’amarin ya faru kuma gaskiya ne, mun samu labarin daga wasu yan kasa nagari cewar abin ya faru a unguwar Gwallamaje.”

DSP Kamal Abubakar yace rundunar ta kama mai asibitin da ma’aikatan asibitin bisa kula da ita ba tare da sanar da hukumar yan sanda ba.

A jiya ne dai wata kotun Abuja ta yanke hukuncin kisa akan Maryam Sanda da ta kashe mijinta, Bilyaminu Bello, tin a shekarar 2017.

UA-131299779-2