Bayan aibata Gadar Lado da Kwankwaso ya taba yi, Gadar Kasa da Kwankwaso yayi ta rurrufta

Gadar kasa da gwamnatin Kwankwaso ta gina a titin Gadon Kaya na jihar Kano ta fara tsagewa.

Hakan yasa aka rufe hannu daya na titin gadar kasar domim riga kafin ruftawa don gudun asarar rayukan al’ummar.

Gwamnatin ta gina gadar ne akan tsabar kudi na Naira miliyan 700.

Kamfanin Rocard Construction Limited ne ya gudanar da aikin.

DABO FM ta bincika cewa fashewar Gadar Kasar da Kwankwaso ta yi, tafi wacce tsohon Sanata Bashir Lado yayi a titin Zaria, wanda ya sa Kwankwaso ya aibata gadar tare da cewa ba tada kyau.

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.