Labarai

Masu Garkuwa sun kashe ‘yar shekara 8 tare da jefa gawarta cikin Rijiya a Kano

Da safiyar ranar Litinin, an tsinci Gawar Aisha Sani, yarinya yar shekara 8 da akayi garkuwa da ita, a cikin wata rijiya dake Tukuntawa, karamar hukumar Kumbotso ta jihar Kano.

Daily Nigerian ta rawaito cewa, wata mata, Hajiya Dije, makociya a kusa da rijiyar da aka tsinci gawar yarinyar ce ta bayyanawa manema labarai cewa; An ga gawar ne dai dai lokacin da ta tura wani yaron dake mata aiki ya debo mata ruwa a rijiyar.

DABO FM tace binciko cewa Hajiya Dije ta shaida cewa; Yaron da ta aika debo ruwan ya dawo a firgice inda ya bayyana mata cewa yaga gawar dan adam tana yawo a kan ruwa.

“Na cewa yaron ya kaini domin na gani da kaina. Zuwa na kenan, sai na gane cewa gawar yarinya ce.”

“Sai nayi ta ihu domin jan hankalin makotanmu. Ba dadewa makotana suka taru, mu ka kirawo ‘yan sanda.” – a cewar Hajiya Dije.

Har zuwa yanzu dai ba’a san suwaye suka kashe Aisha ba.

Yanzu dai haka iyayen yarinyar sun karbi ‘yarsu daga sashin ajiye gawarwaki na asibitin Murtala na jihar Kano.

Wakilin Daily Nigerian ya ziyarci gidansu Aisha dake Santilma a unguwa Birget dake karamar hukumar Nassarawa a jihar Kano.

Da yake bayyana abinda ya faru, mahaifin mamaciyar, Sani Umar, ya bayyana cewa an sace Aisha ne a lokacin da suke dawowa daga makarantar Islamiyya tare da ‘yar uwarta a makon da ya gabata.

Yace yaran suna cikin tafiya ne, wata mata da fuskarta take a rufe da mayafi ta kira ta tare da tambayar sunanta da kuma cewa ta biyota domin suje gidanta.

“‘Yar uwar Aisha tace mata kada ta bita, amma dayake tana da ‘yar matsala a jinta, sai ta bijirewa kiran da ‘yar uwarta tayi mata. Lamarin yasa yar uwarta ta garzayo gida domin sanarda mahaifiyarta abinda ya faru.

“Mahaifiyarta ta kirani don sanar min da abinda ke faruwa. Munyi ta cigiya bamu same ta ba,”

Mallam Umar yace, mako 1 bayan batan Aisha, an aike masa sako wayarshi cewa ya biya kudin fansa na Naira miliyan 10.

Ya kara da cewa, ya fadawa masu garkuwa da mutanen cewa shi bashida wadannan kudaden.

“Kwana 3, suka kara aikemin da sako in bada miliyan 5, nayi musu martanin cewa bani da su.

Daga karshe dai suka bukaci in basu kudi ko nawa ne, na ce musu N80,000 nake da ita.”

Karin Labarai

Masu Alaka

An sace fiye da mutane 60 a Kaduna, mutum 6000 na kan hanyar gudun hijira a jihar

Muhammad Isma’il Makama

Na sace kanwata na nemi kudin fansa miliyan 10 don zuwa kasar waje karatu -Matashi

Muhammad Isma’il Makama

‘Yan Sanda sun samu nasarar bundige Iblis a Najeriya

A nuna wa ‘yan Najeriya gawarwakin masu satar mutane 250 da aka kashe -Shehu Sani

Muhammad Isma’il Makama

Babu inda Boko Haram take da ko taku daya a Najeriya – APC

Muhammad Isma’il Makama

A tantance jami’an tsaro domin ana zargin akwai hannun su a hare hare -Sheikh Sani Jingir

Muhammad Isma’il Makama
UA-131299779-2