Labarai Siyasa

Bayan durkuso da gaisuwar bangirma, alamu sun nuna APC tayi wa Hon Kofa ‘Anti Party’

Rahotanni daga wuraren da ake gudanar da zaben cike gurbin kuri’u na kujerar dan majalissan tarayya na Bebeji/Kiru sun nuna yadda jami’iyyar APC take halin ko in kula da lamarin dan takararta, Abdulmuminu Jibrin.

A makon da ya gabata ne dai aka hangi Hon Abdulmuminu Jibrin ya durkusa har kasa ya gaishe da shugaban APC na Kano, Hon Abdullahi Abbas, ya kuma bude masa mota kafin tafiyarshi.

Tin dai da safiyar yau dinne DABO FM ta tattara cewar jami’an tsaro sun hana Abdulmuminu Kofa takabus wajen zirga-zirga tare da hanashi ganawa da gwamnan Kano, Dr Abdullahi Ganduje.

Shima a nashi bangaren, Hon Kofa ya bayyana rashin jin dadinshi bisa yadda aka gudanar da zaben, sai dai yace zai yi cikakken bayani bayan an kammala zaben da ake gudanarwa a yau.

“Komai ya tafi daidai a nan garin Kofa, mutane sun fito, hukumar zabe ta gudanar da zabe kamar yadda doka ta tanada.

“Duk da bamu san meke faruwa ba, amma mun karbi wasu rahotanni daga wasu mazabun.”

“Duk da dai lokacin bai yi ba da zamu bayyana abinda ya faru ba, amma ana yi abubuwa da ya kaucewa dokar zabe a wasu wuraren.

“Idan an kammala duk abubuwan da akeyi, zan fadawa manema labarai tunani na akan abinda ya faru.”

Hakan na zuwa ne bayan da aka ga Hon Kofa yana tsugunnawa wajen gaishe da shugaban APC na jihar Kano, Hon Abdullahi Abbas, a lokacin da suka sauka a Kano bayan dawowa Abuja wajen shari’ar zaben gwamnan Kano.

Tin dai kwanakin bayan rikici ya barke tsakanin jagororin biyu inda ta kai ga tsige dukkanin yaran da suke goyon bayan Hon Kofa daga shugabancin jami’iyyar APC a kananan hukumomin Bebeji da Kiru.

Masu Alaka

Ganin sabon dan majalisar PDP da ya kayar da Kofa tare da shugaban APC ya jawo cece-kuce

Muhammad Isma’il Makama

APC ta dakatar da Hon Abdulmumin Jibrin Kofa bisa cin amanar Jami’iyya

Dabo Online

Mun sa Kwankwaso ya ajiye siyasa da karfin tuwo – Ganduje

Muhammad Isma’il Makama

Yanzu Yanzu: PDP ta lashe zaben kujerar Abdulmumin Kofa da tazarar kuri’u 35,094

Muhammad Isma’il Makama

Kiru/Bebeji: Baza mu mara wa Kofa baya ba a zaben ranar Asabar -Dattijan APC

Muhammad Isma’il Makama
UA-131299779-2