Turawa sunyi amfani da maganganun PDP wajen saka Najeriya ta 1 a cin hanci -Garba Shehu

Karatun minti 1

Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban kasa ya bayyana cewa da alama rahoton da kunguyar Transparency International (TI) ta fitar wanda ta sanya Najeriya a matsayi na kololuwa wajen cin hanci da rashawa tayi amfani ne da maganganun yan adawa.

Majiyar Dabo FM ta bayyana cewa rahoton na Transparency International (TI) yayi amfani ne da yanda gwamnatin Najeriya ke zabe wajen yaki da cin hanci da rashawa da yanda gwamnatin ke kaiwa gidajen jaridu da yan jarida masu tona rashawa hari a duk sanda suka tona rashawa kamar yadda jaridar TheCable ta rawaito.

Sai dai kuma mukarraban gwamnatin da hukumomin rashawar sun musanta binciken, da yake magana a gidan talabijin na ChannelsTV, Garba Shehu ya ci gaba da cewa “Rahoton hukumar yayi daban da abinda yake a kasa.”

Daga karshe dai Garba Shehu ya karkare da fadin baayi wa gwamnatin tasu adalci baa rahoton cin hanci da rashawa na Transparency International (TI).

Karin Labarai

Sabbi daga Blog