Tabar wiwi na iya zama sahihin maganin da zai kauda cutar Korona -Binciken Masana

Karatun minti 1

Binciken kwararru na hadin gwiwa daga Jami’ar Nebraska tare da Kwalejin binciken halittu ta Texas (Texas Biomedical Research Institute) ya bukaci da a sanya tabar wiwi cikin magunguna da kan iya kauda cutar Kwabid19 daga doron Duniya baki daya.

DABO FM ta rawaito cewa binciken ya kuma bayyana wani sinadari mai suna CDB (Cannabidiol) wanda ke cikin wannan taba ta wiwi da tabbacin zai magance duk wata matsalar huhu da cutar Korona ke haddasawa

Cikin binciken da DABO FM ta gudanar, majiyar mu ta tattara cewa duk da kasar Amurka ta haramta amfani da tabar amma jihohi 29 sun halasta amfani da ita a matsayin magani ciki kuwa harda Washington, DC. Kamar yadda Harvard Medical School ta bayyana.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog