Labarai

Bayan mu’amalar Sanusi da El-Rufa’i, likitoci sun tabbatar Sanusi bashi da Coronavirus

Likitoci sun tabbatar da cewa Muhammadu Sanusi, sarkin Kano mai Murabus tare da iyalinsa basu kamu da cutar Coronavirus ba bayan mu’amala da yayi da gwamnan Kaduna, Nasiru El-Rufa’i.

Majiyar Dabo FM daga TheCable ta bayyana cewa a ranar Asabar aka tabbatar da gwamnan Kaduna, Nasiru El-Rufa’i tare da wani makusancin Sanusi Wanda shima aka tabbatar da ya kamu da cutar.

Dabo FM ta tabbatar da cewa kwanaki 14 da suka wuce tsohon sarkin yayi ganawar sirri tare da chakudedeniya da kuma tafiya cikin Mota guda har ta tsahon awa 4 daga garin Awe dake jihar Nassarawa zuwa babban birnin tarayya dake Abuja.

Karin Labarai

UA-131299779-2