Labarai

Hon Gudaji Kazaure ya baiwa Buhari da gwamnoni shawarar ciyar da al’umma

Hon Muhammad Gudaji Kazaure, yayi kira ga shugaba Muhammadu Buhari da gwamnonin Najeriya da su fito da tsarin ciyar da mutane a lokutan dokar hana zirga-zirga saboda Coronavirus.

Dan majalissar mai wakiltar kananan hukumonin Kazaure, Gwiwa, Roni da ‘Yan kawashi na jhar Jigawa ya bayyana cewa mutanen Najeriya wadanda mafi akasarinsu talakawa zasu shiga cika halin wuya a wannan yanayi na hana zirga-zirga.

Hon Kazaure ya yi wannan kira ne a wani faifan da DABO FM tayi ido hudu dashi wanda dan majalissar ya fita a shafukanshi na sada zumunta.

“Kan batun hana zirga-zirgar a wasu jihohi, Ina kira ga shugaban Najeriya , da taimakon gwamnatin tarayya da ta saka gwamnoni su rabawa mutane abinci da magunguna,”

“Mutane bazasu iya zama ba tare da sun fita yin al’amuransu na yau da kulin ba, dayawa daga cikin mutane suna samun abinda zasu ci a yayin da suka fita a kullin, wasu daga ciki aikin gini suke yi, wasu kura suke turawa.”

“Duk irin wadannan mutanen bazasu iya zama a gida ba tare da iyalansu ba tare da an taimaka musu ba. Don haka nake kira ga gwamnati da ta ba samar da abinci domin ta rabawa mutane a sassan kananan hukumominmu guda 774.”

“Mutane suna shan wahala, idan ka rufe mutane kace bazasu fita ba, kadan ne daga cikinsu zasu iya ciyar da kansu. Yin hakan zai iya kawo abinda yafi Coronavirus, domin yunwa tafi Coronavirus.”

A makon da ya gabata ne shugabancin jami’iyyar APC na mazabar Yamma dake karamar hukumar Kazaure a jihar Jigawa ta ayyana korar Hon Gudaji Kazaure daga jami’iyyar APC.

Korar da a cewar jami’iyyar tayi ne bisa saba dokokin jihar da dan majaliisar yake yi.”

Karin Labarai

Masu Alaka

Ban zagi Buhari ba, ban kuma ce ya gaza ba – Hon Gudaji Kazaure

Dabo Online

APC ta kori Hon Gudaji Kazaure

Dabo Online

Sabon Cajin Banki, fashi da makami ne – Hon Kazaure

Dabo Online
UA-131299779-2