Labarai

Zamu aiko muku da kayyakin da zasu rage radadin zaman gida – Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa gwamnatinshi zata samar da kayyakin rage radadin wanda zasu taimakawa mutane a wannan yanayi na zaman gida.

Shugaban yace a cikin wannan makon gwamnatin za ta fara rabon kayyakin domin saukakawa talaka rayuwa a cikin yanayin da za’a shiga na hana zirga-zirga a wasu jihohin.

“Mutanen da suke rayuwa a unguwanni da wajen gari ko masu zama a wuraen da suke kasuwanci wadanda zasu iya shan wahala a cikin wannan yanayin, da masu rayuwa a garuwan dake kusa da Legas da Abuja, zamu aiko musu da kayayyakin da zasu tallafa musu.”

Shugaban ya sanya dokar hana zirga-zirga a jihohin Legas, Ogun da Abuja na tsawon kwanaki 14.

Shugaban ya bayyana haka ne yayin da yake yi wa ‘yan Najeriya jawabi kai tsaye bisa halin da kasar take ciki game da Coronavirus.

Haka zalika shugaba Muhammadu Buhari yace ya umarci ma’aikatar ayyukan agaji da bala’i domin tattaunawa da gwamnatin jihohi kan yadda za’a fito da hanyar da zata ragewa mutane yunwa, kunci da wahalar da zasu iya shiga yayin dokar hana zirga-zirga.

Shugaban ya kuma bayar da umarnin rufe harkoki da yawo a jihohin Abuja, Ogun da Lagos.

Sai dai shugaban yace kamfanunuwan sarrafa abinci da dillancinsu, asibitoci da duk fanni da ya shafi lafiya zasu iya yin aiki.

Shugaban yace masu kafafen yada labarai ma zasu iya fitowa aiki idan har babu wata hanyar da zasu iya gudanar da ayyukansu a gida.

Karin Labarai

Masu Alaka

Tsohon kwamishinan Kano da ya yi murnar mutuwar Abba Kyari, ya kamu da Koronabairas

Dabo Online

Da dumi-dum: Gwamna Zulum ya kulle iyakokin jihar Borno

Dabo Online

Kwabid-19: Ya kamata gwamnati ta bari koda mutane 12 su yi Sallar Juma’a-Sheikh Comasi

Mu’azu A. Albarkawa

Yanzu yanzu: An samu karin mutum 4 masu dauke da Coronavirus, jumilla 135 a Najeriya

Dangalan Muhammad Aliyu

Jihar Zamfara ta rufe dukkanin iyakokinta don kariyar Coronavirus

Aisha Muhammad

Yanzu yanzu: An samu karin mutane 14 masu dauke da Coronavirus, jumillar 288 a Najeriya

Dabo Online
UA-131299779-2