//
Thursday, April 2

An yaba kokarin Ganduje na karin Naira 600 akan sabon albashin ma’aikata

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Wannan yabo yazo ne biyo bayan kari na Naira har dari shida akan yarjejeniyar dokar mafi karancin albashi.

Rahoton Dabo FM ya bayyana wata kungiya ta ma’aikata a jihar mai suna a turance ‘The Joint Public Service Negotiation Council’ sashin jihar Kano ce ta yi wannan jinjinawa ga Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje.

Kungiyar tace tana yaba biyan sabon albashin na N30,600, inda ta yaba wannan doriya da gwamnan ya kara, da cewa ta haure tsarin dokar ma baki daya.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da ta samu sahalewar mai magana da yawun wannan kungiya, Magaji Inuwa a lanar Laraba, kamar yadda DailyNigerian ta wallafa.

Masu Alaƙa  Aisha Kaita: Shekaran jiya tana PDP, jiya ta shiga APC, yau tayi tsalle ta koma PDP

Tini dai ma’aikata a jihar Kano suka fara sharbar romon dumukradiyyar karin sabon albashin da Gwamnatin jihar Kano tayi.

Karin Labarai

Share.

Comments are closed.

%d bloggers like this:
DABO FM 2020