Xavi Hernandez ya kamu da Koronabairas

Karatun minti 1
Xavi Hernandez mai horaswa a kungiyar Al-Sadd

Tsohon gwarzon dan wasan kungiyar kwallon kafar kungiyar Barcelona kuma mai horar da kungiyar Al-Sadd ta kasar Qatar, Xavi Hernandez ya kamu da cutar Koronabairas, rahotanni sun tabbatar.

Kungiyar ta Al-Sadd ce ta fitar da sanarwar kamuwar dan wasa a shafinta na Instagram a yau Asabar.

Kungiyar ta ce mai horarwarta, Xavi ya ce; “Yau ba zan samu damar kasancewa da ku ba. Mataimaki na, David Prats ne zai jagoranci kungiyar a maimako na.”

“Kwanaki da suka gabata bisa tsarin hukumar gudanar da gasar Lig ta kasar Qatar, sakamakon gwajin cutar Koronabairas da nayi ya nuna cewar na kamu da ita. Duk da ina jin sauki, zan zauna a gida har zuwa lokacin da hukumomi suka sahale min kafin na dawo gareku.”

Sama da mutane miliyan 15 ne suka kamu da cutar a fadin duniya, mutane sama da 640,000 cutar Koronabairas ta kashe a fadin duniya bisa kiduddugar ranar 25 ga watan Yuli, 2020.

Karin Labarai

Dangalan Muhammad Aliyu

•Sublime of Fagge's origin.
•PharmD candidate

Sabbi daga Blog