Labarai

Ba zamu daina nuna shirin Kwana Casa’in ba – Arewa24

Gidan talbijin na Arewa 24 sun bayyana cewar bazasu tsaida haska shirin Kwana Casa’in ba.

Hakan na zuwa ne bayan da hukumar tace fina-finan jihar Kano ta umarci tashar da ta dakatar da haska shirin Kwana Casa’in da Gidan Badamasi.

DABO FM ta tattara cewar gidan talabijin na Arewa 24 sun wallafa sanarwa a shafinsu na Instgram inda suke fadawa masu kallo cewar zasu saki kashi na 2 na shirin Kwana Casa’in a ranar Lahadi mai kamawa.

“Kashi na 2 na shirin Kwana Casa’in, zango na 3, zai zo ranar Lahadi da karfe 8:00 na dare.”

Haka zalika Arewa 24 ta bayyanawa manema labarai cewar hukumar tace fina-finai ba tada ikon hana ta haska fina-finan.

Arewa24 tace dukkanin fina-finan da take haskawa bai sabawa dokar hukumar NBC da take bayar da lasisin tashoshi a Najeriya.

Karin Labarai

UA-131299779-2