Labarai

Hukumar tace fina-finai ta Kano ta dakatar da haska shirin Kwana Casa’in da Gidan Badamasi

Hukumar tace fina-finan jihar Kano da dakatar da tashar Arewa 24 daga haska shirin Kwana Casa’in da gidan Badamasi.

Hukumar da Isma’il Na’abba Afakallah yake jagoranta tace ta dakatar da haska shirye-shiryen ne sakamakon sabawa dokar jihar Kano da fina-finan guda biyu sukayi.

DABO FM ta tattara cewar tin bayan fitowar shirin Kwana Casa’in kashi na 3, akayi ta cece-kuce sakamakon nuna rike-rike da akayiwa mata wanda ake ganin ya sabawa addinin Islama da al’adar Mallam Bahaushe.

A sakon umarni da hukumar ta aikewa gidan talabijin na Arewa 24, tace kada tashar da sake nuna fina-finan guda biyu har sai hukumar ta bata izinin sake haskawa.

“Ina son sanar da kai cewar akwai dokoki dake kunshe a cikin dokar Hukumar tace fina-finai da gyara dabi’u ta jihar Kano.”

“Daga cikin wadannan dokoki nake som janyo hankalinka kan shirin da kuka fitar, a sashin shirin wajen babur mai kafa 3 da kuma sashin da aka hasko a Kantin Sahad, an nuna maza sun rike mace.”

“Wannan ya sabawa addini, al’ada da yanayin rayuwarmu.”

“Daga cikin shirye shiryen da kuka nunawa akwai Gidan Badamasi wanda wanda baku kawowa hukuma shi domin ta tace tare da bayar da izinin haska wa ba, wanda hakan ya sabawa dokar hukuma ta shekarar 2001.”

“Mu baku daga lokacin da takardar nan ta iske ku zuwa awa 48, kada ku sake nuna fim din Kwana Casa’in da Gidan Badamasi sakamakon sabawa dokokin Hukumar Tace Fina-finai ta jihar Kano.

Karin Labarai

Masu Alaka

Arewa24 ta fitar da cigaban shirin ‘Kwana Casa’in’ zango na 2

Dabo Online
UA-131299779-2