//
Thursday, April 2

Bazan bari kuyi zalunci a zaben 2023 ba – Buhari ya fada wa masu madafun iko

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Shugaba Muhammadu Buhari yayi alwashin tsage dantse wajen ganin ba’ayi zalunci a zaben 2023 da za’ayi ba.

Shugaban yayi kira da ‘yan siyasa da suke da ra’ayin fitowa zabe da su jajirce wajen yi wa mutane ayyukan alheri domin bazai bari zalunci ba.

DABO FM ta tattaro shugaba yana bayyana haka yayin da yake karbar manyan jami’an gwamnati da suka zo tayashi murnar cikarshi shekaru 77 a duniya a fadar gwamnatin tarayya dake Abuja.

Shugaban ya gargadi masu shirin yin amfani da jami’an tsaro wajen canja abinda mutane suka fito suka zaba da su kwana da shirin bazai barsu suyi abinda suke so ba.

Karin Labarai

Share.

About Author

Comments are closed.

%d bloggers like this:
DABO FM 2020