Baza’a dena amfani da na’urar Card Reader ba – Hukumar INEC

Babbar hukumar zabe ta kasa INEC ta karyata  wasu zarge-zarge da akeyi mata na shirin dakatar da amfanin da na’urar card reader a zaben gwamnonin da za’a gudanar ranar Asabar 9 ga watan Maris.

Mai magana da yawun hukumar Fetus Okoye ya shaidawa manema labarai cewa basuda wani shiri na dakatar da amfani da na’urarbta Card Reader a zaben gwamnoni dake karatowa.

“Amfani da na’urar ta Card Reader tilas ne domin duk zaben da akayishi babu na’urar bai inganta ba kuma hukumar INEC zata soke shi.”

“Muna jawo hankali mutane da kada su yarda da irin wadannan maganganun domin duk karyace wacce batada tushe ko kadan.”

Masu Alaƙa  INEC ta kwace takarda shaidar cin zabe daga 'dan majalissar APC a jihar Ondo

 

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.