Bincike Labarai

Bincike ya nuna fiye da kashi 75% na matan Najeriya suna amfani da mayuka da allurar bilicin

Wasu kwararru a fannin hada man da yake canja launin yadda fata take sun bayyana cewar lallai yin amfani da su nau’oin wadannan mai na da matukar hadari ga lafiyar mutum.

Binciken yace yanzu mata da masu yin haka sun fi yin amafani da Allura ne da ke kunshe da ‘Glutathione’.

Duk da  cewar su masanan  sun ce akan samu kwayar ‘Glutathione’ a cikin jikin mutum kuma yana taimakawa wajen kara karfin garkuwan jiki da hana mutum kamuwa da cututtuka.

Bayan haka kuma shi wannan sinadari na canja launin fatar mutum da kuma kawar da tabo idan yana da shi.

Shi dai kokarin canja launin fata bai tsaya ga mata ba kawai a wannan zamani domin har maza ma suna yin haka.

A rahoton da Dabo FM ta samo wanda jaridar Leadership ta rawaito wata mata da ta kware a hada man ire-iren wadannan mai dake kasuwar Wuse a Abuja tace ta jima tana yin wannan harkar .

Mrs Haruna ta bayyana cewar duk da  mutane sun fi yin amfani da kwayoyi da yin alluran ‘Glutathione’ har yanzu wasu na amfani da na mai ne cewa babban dalili kuwa shine don irin tsadar da kwayoyi da allura su ke da shi,Tace ita nata man nada arha matuka.

Karin Labarai

UA-131299779-2