//
Tuesday, April 7

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta kama wata mota da aka sato daga Kano

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Rundunar yan sandan ta jihar Katsina ta damke wani mutum mai suna Ibrahim Usman mai shekaru 35 mazaunin unguwar Kwari dake yankin Badawa a nan Kano, bisa zargin sa da satar mota.

Mutumin ya bayyanawa ‘yan sanda cewa ya sato motar ne daga wani kamfani dake Titin Audu Bako a nan birnin Kano.

‘Yan sanda sun kama Ibrahim Usman a lokacin da yake kokarin fita da motar kirar Toyota mai daukan mutane 35 zuwa kasar Nijar ta jihar Katsina.

A wata zantawa da gidan radiyon Dala tayi da kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Katsina SP Isah Gambo wanda ya tabbatar masa da faruwar al’amarin, inda ya ce rundunar su ta kara samun nasarar cafke wasu gun-gun matasa da suka addabi birnin Katsina da sace-sace.

Karin Labarai

Share.

Comments are closed.

%d bloggers like this:
DABO FM 2020