A kalla sojojin Najeriya 20 da farar hulla sama da 40 ne suka rasa rayukansu a hare-hare guda biyu da kungiyar Boko Haram ta dauki alhakin kai wa a ranar Asabar, mazauna garuruwa da wani jami’in tsaro suka tabbatar.
Hakan na zuwa ne kwanaki kadan bayan da mayakan ta’addancin suka kashe mutane 81 a wani mummunan hari da suka kai a kauyen Gubio na jihar Borno.
Ma’aikatan ayyukan jin kai guda 2 da mazauna garuruwan sun shaidawa kamfanin Reuters cewar mayakan kungiyar dauke da muggan makaman da suka hada da Makamin Roka sun shiga garin Monguno, matattarar kungiyoyin bada agaji masu zaman kansu da misalin karfe 11 na safiyar Asabar.
Mayakan kungiyar sun mamaye jami’an tsaro na gwamnati, suka jikkatasu tare da kashe a kalla dakarun soji 20 suka yi ta shawagi har tsawo awanni 3.
Majiyoyin sun sake tabbatarwa da Reuters cewar harin ya raunata daruruwan fararen hula, lamarin da ya sanya asibitoci a yankunan sukayi cikar kwari tare da samun wasu a kwacen a kofar asibitocin suna jiran tsammani.
Kazalika Reuters ta rawaici cewar mayakan Boko Haram sun kone ofishin ayyukan jinkai na majalissar dinkin duniya tare da cinnawa ofishin ‘yan sanda a yankunan wuta. Mayakan sun kuma rarraba takardu na kashedi ga mazauna yanki akan kada su sake su yi ayyukan hadin gwiwa da jami’an tsaro ko kungiyoyin bayar da agaji.
Mayakan sun shiga garin Nganzai da misalin karfe 11 na safe, kamar yadda mazauna gari da wani jami’in CJTF suka tabbatar. Sun shiga garin a kan babura da motoci inda suka kashe sama da mutane 40, kamar yadda majiyoyin suka tabbatarwa Reuters.
Ko da aka tuntubi mai magana da rundunar sojin, ba a iya samunshi domin bai dauki kiran ba.
