Tin bayan da gwamnanan jihar Kano, Dr Abdullahi Ganduje ya amince da bude gidajen kallon kwallon kafa a jihar, al’ummar ciki da wajen jihar suke da cece-kuce.
DABO FM ta tattara cewar a ranar Juma’a gwamnatin jihar Kano ta amince da bude gidajen kallon kwallon kafa a fadin jihar Kano bayan ganawa da shugabannin masu gidajen kallon a jihar.
Sai dai zancen bude gidajen kallon bai yi wa al’ummar jihar dadi ba musamman magidanta sakamakon rashin bude makarantun Islamiyya a fadin jihar.
Wani mai fashin baƙi a al’amuran yau da kullin, Muhammad Sulaiman Abdullahi ya bayyana bude gidajen kallon da gwamnatin tayi a matsayin rashin sanin abinda ya kamata.
“Yawanci shugabanninmu ba sa tunani mai kyau kuma basu da mutanen kwarai da zasu fada musu yadda za su yi abu mai kyau. Wadanda ma suke aiki a matsayin masu basu shawara sun zaman ‘yan amshin shata tare da zama masu karbar umarnin duk abinda shugaban ya zo musu da shi.”
“Kada ma ayi kokarin yi min banayin hujjar da ke tattare da bude gidajen kallon, ba zan gane ba. Har yaushe muka gama maganar a bar mu muyi Sallah.
“Za a iya cewa; na farko, kun fara abin fara bi rukuni-rukuni, wannan haka bane. Wana rukuni ne yafi na makarantun Islamiyya? Meyasa aka bai wa shaidanci fifiko sama da Musulunci? Meyasa har yanzu makarantunmu na Islamiyya da na Boko suke a rufe?
“Na biyu, za a iya cewa, manya ne suke zuwa gidajen kallo. Wannan karya ne kuma shima ba haka bane. Idan da gaske kuma za ayi adalci sai kace makarantun Islamiyya na manya su koma idan kana so ka nuna kulawarka ta bogi ga yaranmu kana na.
“An fada mana cewa mafi yawan masu gidajen kallon nan duk ‘yan siyasa ne, wasu kuma su na bai wa gwamnati kudi wanda gwamnati ke ganin su kamar kudaden shiga.”
“Mu bamu da abinda zamu baka, ka bude mana Islamiyoyinmu kawai. Addu’a kadai zamu yi ta Allah Ya shiryeku kuma mu cigaba da karanta Al-Kur’ani. Ko da haka zaka amfana.
