Labarai

Buhari ya amince da bukatar kamfanin Hyundai na fara kera Motoci a Najeriya

Shugaba Buhari ya bayyana cewa zasu hana hannu tare da bawa kamfanin Hyundai damar fara kera motoci tare da gyaran matatun mai Najeriya.

DABO FM ta tattara cewa shugaba Buhari ya bayyana haka ne yayin da yake karbar shugaban kamfanin, Mista Chang Hag, a fadar gwamnatin tarayya dake Abuja.

Shugaban yace; “A yanayin da ake ciki, Najeriya ta sanya samun abubuwa na kashin kanta wanda zuwa yanzu abinda muke fatan shine zuwa shekaru 3 masu zuwa ya zamana muna da isasshen tacaccen mai da zai ishemu.”

A wata sanarwar da mataimakin shugaban a fannin labarai, Femi Adesina ya fitar, yace shugaba Buhari ya karbi bukatar kamfanin Hyundai domin kafa kamfaninsu a Najeriya. “Zamu samar da dukkanin abinda ake bukata domin wanzar da hakan.”

Shima a nashi bangaren, shugaba kamfanin, ya bayyana yacce kamfanin yake son bawa Najeriya gudunmawa wajen habbaka tattalin arzikin kasar.

“Mun dade muna gina matatun mai a fadin duniya. Muna da wacce tafi kowacce girma cikin duniya a kasar Koriya ta Kudu.”

“Muna nan a kasar Venizuwala, Iraki da sauran kasashe masu yawa, zamuyi matukar farinciki yada wani zangon namu a Najeriya.”

Karin Labarai

UA-131299779-2