//
Wednesday, April 1

Kotun koli ta kori hukuncin kotun daukaka kara, ta tabbatar da gwamnan PDP

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Kotun kolin Najeriya ta kori hukuncin kotun daukaka kara na zaben gwamnan jihar Oyo, ta tabbatar da gwamnan Makinde a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar.

Kotun wacce ta zauna yau Laraba, 18 ga watan Disamba, ta yi watsi da shari’ar kotun daukaka kara tayi a watan Nuwamba.

Sashin Hausa na Legit ya tattara cewa a ranar 11 ga Nuwamba, kotun daukaka kara da ke zama a Ibadan, babbar birnin jihar Oyo ta soke zaben Gwamna Seyi Makinde na jihar.

Kotun ta yanke hukunci ne a karar da Adelabu na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ya daukaka. Kotun ta dage hukuncin kotun sauraron karar zabe wacce ta jaddada nasarar Makinde.

Masu Alaƙa  Da Dumi Dumi: Rarara ya saki sabuwar waka tun gabanin hukuncin kotun koli

Sai dai kuma, kotun ba ta kaddamar da Adelabu a matsayin wanda ya yi nasara ba.

Duk da umurnin kotun, gwamnan Seyi Makinde ya cigaba da kasancewa gwamna zuwa yanzu kotun koli ta yanke hukunci na karshe.

Karin Labarai

Share.

About Author

Comments are closed.

%d bloggers like this:
DABO FM 2020