Shugaba Muhammadu Buhari ya bayar da umarnin daukar ma’aikata 774,00 domin taimakawa wajen yaki da cutar Kwobid-19 a Najeriya.
Ministar Kudi, Zainab Ahmad ce ta bayyana haka yayin wata ganawa da manema labarai yau Litinin a birnin tarayyar Abuja akan matakan kariya da gwamnatin tarayya take dauka wajen kare kasar daga annobar Kwobid-19.
Ministar ta bayyana cewar za a dauki mutane 1000 a kowacce karamar hukuma dake fadin Najeriya guda 774.
Ta kara da cewa gwamnatin ta ware kimanin Naira biliyan 60 domin biyan alawus na ma’aikatan da za a dauka tare da tabbatar da ayyukan sun tafi yadda aka tsara.
Haka zalika tace gwamnatin ta ware Naira biliyan 500 a matsayin kudaden da za a kashe biyo bayan ballewar annobar, kamar yadda kamfanin dillancin Najeriya na NAN ya fitar.
“An ware biliyan 500 domin ingantawa da gyaran fannin lafiya.”
