Shugaba Muhammadu Buhari ya bada umarni da a rabar da motocin Shinkafa 150 da hukumar hana fasa kwauri ta karbe.
Shugaban yace a rarraba shinkafar zuwa jihohin Najeriya 36.
Ministar kudi, Zainab Ahmad ce ta sanar da haka yayin wata tattaunawarta da manema labarai a birnin Abuja akan kokarin da gwamnatin tarayya take yi kawar da cutar Kwabid-19.
Ministar tace tini dai aka aike da motocin shinkafar zuwa ma’aikatar ayyukan jin kai da bala’i domin a rabar da shinkafar zuwa ga ‘yan Najeriya.
Haka zalika tace shugaban ya bayar da umarnin rabawa al’ummar Najeriya hatsi da yake a rumbin gwamnati.
Duk dai a shirin da gwamnatin tace tana yi wajen saukaka harkar noma, Haj Zainab tace shugaba Buhari ya bayar da umarnin siyar da buhun taki akan N5000, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Najeriya ya fitar.
