Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari
Labarai

Buhari ya fitar da sanarwar daukan nauyin karatun dalibai 3

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya dauki nauyin karatun wasu ‘yan makarantar sakandare guda 3 tin daga digiri fari har zuwa digirin digirgir ‘Doctorate Degree’.

Majiyar Dabo FM ta bayyana wannan ya biyo bayan samun nasarar da daliban 3 sukayi wajen gasar ‘The 2020 Young Nigerian Scientists Presidential Award Competition.’ Wato gasar kimiyyar kankanan ‘yan Najeriya wanda shugaban kasa ya tsara.

Wannan daukan nauyin na nufin an yassare musu zuwa kowacce jami’ar a fadin Najeriya domin yin kowanne karatu da suke so na kimiyyah. Kamar yadda jaridar TheGuardian ta fitar.

Daliban sune Akintade Abdullahi-Akanbi na makarantar Government High School Osogbo; Uwakwe Nelson-Kamsiyochukwu, daga British Spring College, Awka, Sai kuma Aimofumhe Eshiobomhe-Sigmus of School of the Gifted, Gwagwalada, Abuja.

Daga karshe ministan kimiyya, Dr Ogbonnaya Onu yayi shugaban kasa, Muhammadu Buhari godiyar wannan hobbasa da yayi.

UA-131299779-2