Labarai

Ganduje zai samu gagarumar lambar girmamawa daga fadar shugaban kasa, Buhari

Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje na daga cikin wadanda zaa karrama a wani gagarumin biki da zaai a watan gobe April a fadar shugaban kasa Muhammad Buhari.

Majiyar Dabo FM a wata sanarwa da taimakwa gwamna wajen yada labarai, Salihu Tanko Yakasai ya fitar a ranar Alhamis 18 ga Mayu, ya bayyana gwamna Ganduje ya gana da kwamitin duba aiyukan tabbatar da muradun karni na kasa wato SDGs wanda kuma shine ke shirya bikin bada lambar girma ga jihohi da maaikatun da sukai fice a harkar tabbatar da muradun karni wato SDGs a Najeriya.


Kwamitin mai mutum 7 wanda yake karkashin Jagorancin Dr. Ibrahim Albashir na da membobi da suka kumshi wakilai daga ofishin Fadar Shugaban Kasa, da kuma ofishin mai bashi shawara akan muradun karni da sauran masu ruwa da tsaki a fanni.

Yakasai ya kara da cewa Gwamnatin Ganduje ta yi fice wajen ganin ta cika kaidojin tabbatar da muradun karnin inda ta taka rawar gani sosai a fannin, kuma bisa haka ne aka zabi Gwamna Ganduje a cikin wadanda zaa karrama a wani gagarumin biki da zaai a watan gobe April a fadar shugaban kasa Muhammad Buhari.

A cikin wanda suke tare da Gwamna akwai mai bashi shawara akan harkokin tabbatar da muradun karni wato Special Adviser on SDGs Hon Habib Hotoro.

Hoto daga Salihu Tanko Yakasai

UA-131299779-2