Labarai

Coronavirus: Kasar Saudiyya ta dakatar da sallar Juma’a

Kasar Saudiyya ta dakatar da taruwa wajen sallar Juma’a domin gudun kamuwa da cutar ‘Coronavirus’.

Majiyar DABO FM ta rawaito majilisar sarakuna Kasar ce ta fitar da sanarwar domin dakile yaduwar cutar a wani taron tattaunawa a babban birnin Kasar dake Riyadh a ranar Talata.

Majiyar tamu daga jaridar TheCable ta bayyana cewa dokar zatayi aiki ne a ko Ina cikin fadin Kasar banda massatai guda biyu, wato na Makkah dana Madina.

Tundai bayan bullar cutar tayi sanadiyyar mituwar daruruwan mutana a fadin duniya.

UA-131299779-2