Shugaba Muhammadu Buhari ya sanya hannu kan dokar da zata haramtawa gwamonin jihohi rike kudaden majalissar jiha da kuma bangaren shari’a ta jiha.
Shugaban ya sanar da haka ne a shafukansji na sada zumunta a yau Juma’a, 22 ga watan Mayun 2020.
Based on the power vested in me under Section 5 of the 1999 Constitution (as Amended), I, today, signed into law Executive Order No. 10 of 2020 for the implementation of Financial Autonomy of State Legislature and State Judiciary.
— Muhammadu Buhari (@MBuhari) May 22, 2020
Kazalika, babban mai mataimakin sakataren babban mai shari’a na kasa, Dr Umar Jibrilu Gwandu ya sanar wa da manema labarai haka a osifishinsu dake babban birnin tarayyar Najeriya.
Sanarwa tace an sanya dokar ne bisa sashin doka ta 121(3) na kundin tsarin mulkin Najeriya da aka samar na cin gashin bangaren shari’a da ‘yan majalissu wajen yin al’amuran kudadensu da kansu.
Haka zalika sanarwar tace sabuwar dokar za ta bai wa bangarorin mulkin damar aiwatar da ayyukansu cikin ‘yanci tare da samun damar bincikarsu akan yadda suke kashe kudade.
Dokar ta ce daga rana mai kama ta yau, babu wani gwamna ta zai rike kudin bangarorin mulkin guda biyu.
Bisa sashi na 121(3) na kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999 (Gyara) yace tilas ne kowacce gwamnatin jiha ta ware hakkin dukkanin bangarorin guda biyu ba tare da bijiro da wata bukata akan kudin ba.
Duk dai a cikin sanarwar, dokar ta ce za a fitar da kudade masu yawa a cikin shekaru 3 na farko da fara aiwatar da dokar domin a bai wa bangaren shari’a domin suyi gyara tare da yin ayyukan cigaba a zauren kotunansu da suka hada har da na Musulunci da na daukaka kara.
