Buhari ya tsige Amaechi

Shugaba Muhammadu Buhari ya tsige ministan harkar sufurin Najeriya daga mukaminshi na daraktan yaƙin neman zaben shugaba Buharin.

Senator Bola Ahmed Tinubu, shi shugaba Buharin ya nada a matsayin mai jan ragamar yaƙi neman zabenshi na 2019.

Hakan na zuwa ne kwanaki kadan da masu fafutukar yaƙin neman zaben Atiku Abubakar suka fitar da wani sautin muryar da sukayi iƙirari da Ministan sufurin yayi wasu kalamai da suka nuna gazawar gwamnatin da shugaba Buharin ke

jagoranta.

Zaben da za’a gudanar a kwanaki kasa da kwana arba’in yana cigaba da jan hankulan kasashen duniya don ganin yacce zata kaya.

Masu Alaƙa  Buhari ya tsige Amaechi

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.