/

Ba mu ba APC – Rochas

Karatun minti 1

Gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha ya ce al’ummar jihar Imo za su zabi shugaba Muhammadu Buhari a matakin shugaban kasa amma a zaben gwamna su da APC sun yi hannun riga.

Gwamnan ya yi wannan kalamai ne a taron yakin neman zaben matasa da mata wanda uwargidan shugaba Muhammad Buhari ke jagoranta.

Za mu zabi Buhari a zaben shugaban kasa amma zaben gwamna ba za mu zabi APC ba domin ba za a mana tushen dan takara na babu gaira babu dalili ba. Kuma mun riga mun yanke shawararmu a haka.

A jawabin nata, uwar gidan shugaba Muhammad Buhari, Haj Aishat Muhammadu Buhari wacce ta samu wakilcin uwargidan mataimakin shugaban kasar , Oludolapo Osinbajo tayi kira ga matasan da su tabbata sun zabi jam’iyyar APC domin cigaba da samun cigaba a kasa.

Wannan taro shine irinshi na farko da aka gudanar a jihar ta Imo.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog