Tue. Nov 19th, 2019

Dabo FM Online

World’s First pure Hausa online Radio

Akwai matsala a Najeriyar da ‘yan siyasar neman duniya suke jagoranta – Dauda Dangalan

2 min read

Dattijo Alhaji Muhammadu Dauda Dangalan, dan gwagwarmaya a jami’iyyar NEPU, PRP da PDP, ya bayyana cewa akwai abin damuwa da takaici a sha’anin mulkin Najeriya duba da yadda masu madafun iko suka fi damuwa da kudi akan mutane da kasar da suke mulka.

Dauda Dangalan ya bayyana haka ne yayin wata ganawa da yayi da jaridar Daily Trust a ofishin shi dake Lamba ta 2, gidan Abdullahi dake kan titin Katsina a birnin Kano.

Da yake amsa tambayar wakilin jaridar cewa, Ta yaya zaka kwatanta siyasar lokacin ku na, NEPU da PRP da kuma siyasar wannan zamanin?

Ya amsa da cewa, “Ina jin bakin cikin siyasar yanzu ta yacce ‘yan siyasar suka tsunduma cikin siyasar kudi. Abin takaicin ma shine yacce matasan yan siyasa sukayi fi bawa kudi da mukaman da suke muhimmanci fiye da mutane da kuma kasar su.

Wacce irin makoma muke ginawa kanmu kenan?

“A ganina, an yaudari matasa kan cewa siyasar kudi abune mai kyau tare da cusa musu akidar cewar itace hanya mafi kyau wajen aiwatar da abubuwa.”

Ina jin ba dadi, kuma zai ta zama a rai na har karshen rayuwa ta. Akwai ban takaici da bacin rai a yanzu, idan ka duba, a masu mulki, babu batun soyayya da kishin kasa, abune mai wahala a samu.”

©2019 Dabo FM Online. Sponsored by Dabo Media Group | Newsphere by AF themes.