Bulama, ya bukaci EFFC ta bayyanawa duniya gaskiyar data gano akan bidiyon Ganduje

Lauya mai rajin kare hakkin ‘dan adam, Audu Bulama Bukarti ya aikewa hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFFC sakon neman bayanai akan hakikanin gaskiyar bidiyon gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje wanda jaridar Daily Nigerian ta fitar.

A sakon daya aikawa shugaban hukumar, Ibrahim Magu ya bukaci hukumar da ta bayyana ina aka kwana akan maganar bidiyon, ya kuma kara da cewa ya rubuta wasikar ne saboda maganar da Magu yayi na cewa yana birnin Landan domin bincikar bidiyon.

Wata majiyar sirri tace binciken hukumar ya tabbatar da ingancin bidiyon amma ba’a bayyanawa al’umma kasa ba saboda wasu dalilai na siyasa, wadanda zasu iya kaiwa ga shugaba Muhammadu Buhari rasa samun kuri’ar mutanen Kano.

Masu Alaƙa  Gwamnatin Kano ta dauki kwararru don koyawa Matasan jihar Sana’o’i

Ya kuma bukaci hukumar data fitar da bayanan a cikin kwana 7, kamar yacce dokikin kasa suka bashi dama.

A watan Oktobar shekarar 2018 ne jaridar Daily Nigerian ta saki bidiyoyin da suka nuna gwamnan jihar Kano, Ganduje yana loda samfurin kudi na dalar Amurka a cikin aljihun babbar rigarshi. Kudin da ake zargin ya karbesu daga wajen dan kwangila, wanda adadinsu yakai $5m.

Wasikar da Bulama Bukarti ya aikewa hukumar EFCC

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.