/

Kwankwasiyya ta maka Ganduje a kotu domin hana shi ciyo bashin Biliyan 300

Karatun minti 1

Kungiyar kwankwasiyya ta maka gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje a kotu domin hana shi ciwo bashin €684,100,100.00 a wani banki na kasar Sin, China Development Bank.

Rahoton DABO FM ya bayyana gwamnatin jihar Kano na son karbo bashin ne domin fara harkar sufurin jiragen kasa.

An aike da kwafin wannan kara zuwa majalisar jiha, ofishin shugaban majalisar dattijai, ma’aikatar kudi ta kasa, Hukumar bada bashi, Ofishin jakadancin kasar Sin da Bankin da ake shirin karbar wannan bashi, Chinese Development Bank.

Sanarwar ta fito ne daga dan takarar mataimakin gwamna a zaben 2019, Kwamared Aminu Abdulsalam, wanda ya bayyana “Daga karshe kudin zasu fada cikin aljihun babbar rigar gwamna ne kawai.” Kamar yadda DailyNigerian ta fitar.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog