Galadiman Kano ya cika shekara biyar da rasuwa

dakikun karantawa

Tarihin Marigayi Galadiman Kano Alhaji Tijjani Hashim.

An haifi Galadiman Kano Ahmadu Tijjani dan Turakin Kano Hashimu, dan Sarkin Kano Abbas, dan Sarkin Kano Abdullahi, dan Sarkin Kano Ibrahim Dabo a shekarar 1932 a cikin birnin Kano.

Ya fara karatun elementare a garin Bebeji a shekarar 1944. A shekarar 1944 ya shiga makarantar Medil ta Kano inda ya daina a 1951.

A 1952 ya fara aiki a NA ta Kano da mukamin Malamin Dabbobi, mai duba tsaftar dabbobi da za’a yanka a kara ta Kano. A 1956 aka zabe shi dan majalisa mai wakiltar Sumaila a majalisar dokoki ta Arewa.

A zaman sa a wannan majalisa ne ya rike mukamai da dama kamar shugaban hukumar bada kwangila ta Kaduna da shugaban kwamitin tabbatar da jam’iyyar NPC ta lashe zabe a lardin Sardauna. Ministan cikin gida na Jihar Arewa. Kwamishinan lardi mai kula da Lardin Kabba wadda akan wannan mukami soja suka yi juyin mulki. Dawowarsa gida ne tasa Sarkin Kano Marigayi Ado Bayero, ya nada shi sarautar Dan Isan Kano kuma kansila mai kula da ayyukan gayya da taimakon kai da kai.

A 1976 ya sami karin girma zuwa sarautar Turakin Kano da bashi kulawa da gundumar Kumbotso. A 1980, ya sami canji zuwa kansila mara ofis saboda yawan harkokinsa. A 1989, ya sami karin girma zuwa sarautar Dan Iyan Kano da ci gaba da rike mukamin kansila mara ofis.

A 1992, ya sami karin girma a babbar sarautar Kano a matsayin Galadiman Kano kuma shugaban kwamitin kudi na majalisar Sarki. A 2012 Sarki ya kara masa aikin hakimcin birnin Kano.

“Galadiman Kano Tijjani mashahurin mutum ne da babu irin sa a wannan zamani wajen taimako, adalci, tausayi da kyautatawa. Shi kadai ne a wannan zamani mai sarauta attajiri mashahuri Kasaitacce da za ka je gurinsa har ka tadda shi ba mai tambayar ka ina za ka”.

Allah ka dube shi, Kayi masa Rahma ka tausaya masa Ka jikansa, Ka sa Aljanna ce makomarsa. Ameen.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog