Sojojin kasar Chadi

Chadi ta janye Sojojinta 1200 dake taya Najeriya yakar Boko Haram

Rundunar Sojin kasar Chadi ta janye dakarunta kimanin guda 1200 dake taya Sojojin Najeriya yakar mayakan kungiyar ‘yan ta’addar Boko Haram.

Kanar Azem Bermandoa, kakakin rundunar sojin kasar Chadi ne ya bayyanawa gidan jaridar AFP janyewar dakarun kasar daga Najeriya.

“Sojojinmu ne suke dawo gida yanzu tin bayan da muka turasu kai wa Najeriya agaji a watannin da suka gabata.” – Cewar Kanar Azem Bermandoa.

Ya bayyana cewa zuwa yanzu babu wani Sojan kasar da ya rage a Najeriya, kamar yacce AFP ta tabbatar.

“Wadanda suka dawo, zasu koma bangarensu na ‘Lake Chad'”

Haka zalika shugaban Sojojin na kasar Chadi ya bayyana cewa a shirye suke da sake turawa duk wata kasa a yankin Tafkin Chadi da ta bayar da gudunmawa wajen hada dakarun yaki da ‘yan ta’adi, sojojinsu indai an cika ka’iodoji.

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.