34 Qur'anin Graduation Nigeria
Labarai

Yanzu-Yanzu: Jihohin Kano da Kaduna sun lashe Musabakar karatun Al-Kur’ani ta Najeriya

Dan jihar Kaduna, Umar Kabiru ya zama gwarzon shekara a musabakar karatun Al-Kur’ani ta Najeriya (Rukunin Maza), haka zalika Diya’atu Sani Abdulkadir, ‘yar jihar Kano ta zama gwarzuwar shekara a musabakar da aka kammala yau Asabar a jihar Legas.

Kwamitin Musabakar Al-Kur’ani ta Najeriya da cibiyar Addinin Musulunci dake jami’ar Usmanu Dan Fodio suka shirya tare da hadin gwiwar al’ummar musulmin jihar Legas ne suka shirya Musabakar.

Musabakar da mai alfarma Sarkin Musulmi, Sultan Sa’adu Abubakar, ya bude ta jiya Juma’a a garin Legas, ta kammalu a yau Asabar.

DABO FM ta tattaro cewa bayan kammala musabakar, wadanda suka lashe sun fito filin taron da sabbin motocin da aka basu kirar Almera ta kamfanin Nissan da sauran kyaututtuka.

An dai raba rukunin musabakar zuwa kashi 6 wanda ya hada da Rukunin da suka haddace Kur’anin baki daya tare da Tajawidi da Tafsiri a aikace da Ilmance da kuma rukunin Haddar Al-Kur’ani sukutum da Tajawidi kadai da kuma rukunin haddar izifi 40 da Tajawidi a aikace.

Sauran rukunin ya hada rukunin haddar izifi 20 da Tajawidi a aikace da ilmance, rukunin izifi 10 da Tangimi a aikace da Tajawidi a ilmance da kuma izifin Amma ko kowanne daga cikin ragowar izifi da Tajawidi a aikace.

Shehun Borno, mai girma Abubakar Ibn Umar Garbai EL-Kanemi ne ya nada Umar Kabir a matsayin gwarzon ya lashe rukunin izifi 60, a yayin da uwargidan gwamnan jihar Legas, Hajiya Khadija Hamza ce ta bawa ‘yar jihar Kano da ta zama garzuwar shekara kambunta.

Wanne ne karo na 34 da ake shirya irin wannan gagarumar musabaka a Najeriya.

Karin Labarai

Masu Alaka

Sarkin Musulmi, Sheikh Ibrahim Saleh da Buhari sun shiga sahun Musulmai 500 masu fada-a-ji a duniya

Dabo Online

Sarkin Musulmi da Sheikh Sharif Saleh sun shiga sahun Musulmai 500 masu fada-a-ji a duniya

Dabo Online
UA-131299779-2