Labarai

Cibiyar Cfloahra ta kaiwa Sarkin Zazzau Ziyara

A kokarin ta na cigaba da kyautata dangantaka tsakanin ta da shuwagabannin al’umma, cibiyar fadakar da al’umma game da dokoki da taimakon Dan Adam wato Center for Legal Orientation and Humanitarian Aid (Cfloahra) a turance. ta kai ziyarar ban girma ga Mai Martaba Sarkin Zazzau kuma shugaban majalisar sarakunan Jihar Kaduna a fadar sa da ke Zariya.

Da yake bayyana da makasudin zuwan su fadar, shugaban cibiyar na kasa Kwamared Mustapha Sa’id Kano, ya ce, cibiyar ta su ta jima tana bada taimakon musamman ga mata da sauran al’umma, domin bunkasa rayuwar su da cigaban su. Sannan ya ce, yanzu haka sun bullo da wani shiri da ke da manufar taimakawa mata da audugan kariya lokacin da suke gudanar da al’adar su ta wata-wata.
Kuma manufar Shirin shi ne ganin yadda mata kan shiga halin ni’iyasu a lokutan da suka tsinci kansu a wani yanayi

A cewar shi, suna da manufar fadada ayyukan su, ta hanyar shiga yankunan karkara wanda hakan ba zai samu ba sai da samun hadin kan sarakunan gargajiya domin kaiwa ga gaci.

Ya kara da cewa, a matsayin mai Martaba uba ga al’ummar Najeriya baki daya, suna rokon ya kasance jigo da zai shige gaba wurin tallafawa shirin nasu da shawar-wari da kuma dukkanin abubuwan da suka dace domin ta sanu a fadin Jihar Kaduna.

Kwamared Mustapha Sa’id ya kuma taya Mai Martaban murnar cika shekaru 45 bisa karagar mulkin Zazzau, sannan ya yi fatan karin shekaru masu albarka a nan gaba.

Da yake maida jawabi, Mai Martaba Zazzau Alhaji Shehu Idris, ya nuna matukar farin cikin sa ne da ziyarar da kungiyar ta kawo masa. kuma ya ce, ganin kusan dukkanin membobin kungiyar matasa ne, ya sa shi da majalisar sa, za su tsayu wurin tallata manufofin kungiyar domin kaiwa ga tudun mun tsira.

“Ina da tabbacin hadin kan matasa da na gani, zai taimaka wurin kawar da sha da kuma fataucin miyagun kwayoyi tsakanin matasa”, inji Sarkin na Zazzau.

Ya hori membobin kungiyar su zama masu sanya kishin kasa a gaban su saboda ta haka ne za su taimaka wa manufofin gwamnati akan matasa.

A karshe shugaban kungiyar na kasa Kwamared Mustapha Sa’idu ya rantsar da sabbin shuwagabannin kungiyar reshen Jihar Kaduna tare da basu takardar shedar kama aiki.

Karin Labarai

UA-131299779-2