Labarai

‘Ungozoma’ ta yanke wa mijinta Harshe da Hanci, ta kira Surukarta ta dauki gawa

A jihar Imo, an kwantar da wani babban likita mai sunan Cherechi Okonko a sashin bayar da agajin gaggawa na gwamnatin tarayyar Najeriya dake garin Owerri sakamakon raunuka da mai dakinshi tayi masa.

Kamar yadda PUNCH ta bayyana, matar likitan a matsayin ungozoma ta cire wa mijinta nata hakwaran saman baki tare da cire masa iyakar harshe dake iya fitowa daga baki da wani sashen ganda.

PUNCH ta tattara cewar tini dai aka garzaya da likitan zuwa asibiti yayin da yake a yanayin da bai san inda kanshi yake ba.

Mijin ungozomar ya kasance a likitan sha’anin Mata dake aiki cibiyar lafiya ta tarayya dake Owerri.

Wani ma’aikacin a asibitin da ya bukaci a boye sunanshi ya bayyana cewar; “Uwarigidan wani wani likitan cibiyar kiwon lafiya ta ji masa rauni mai muni bayan sa-in-sa tsakaninshi da matarshi.

Yace; “matar ta yanke masa hanci, hakwaranshi na sama, gaban harshenshi da wani sashe na ganda a cikin bakinshi. Ta kuma kira mahaifiyarshi tace tazo ta dauki gawar ‘danta.

“Likitan ya taki sa’a, an garzaya da shi zuwa asibiti da gaggawa a cikin dare inda aka samu kanshi. Duk da ya samu kanshi, har kawo yanzu baya iya magana.

Kakkain yan sandan jihar ya bayyana har yanzu labarin bai iske rundunar ba.

Karin Labarai

Masu Alaka

Da suwa Hanan take tarayya wajen ture-turen hotuna da maganganin batsa?

Dabo Online

Budurwa ta rasa ran ta bayan amfani da ‘Maganin kashe kwari’ don cire kwarkwata

Dabo Online

Habib4u: Dattijon daya bukaci Hanan ta tura masa hotonta mai motsa sha’awa

Dabo Online

Maryam Sanda ta tsere bayan Kotu ta tabbatar da kisan da tayi wa mijinta

Dabo Online

Budurwa ta caccakawa Saurayinta na daduro wuka a jihar Legas

Dabo Online

Tsananin kishi ya sanya wata mata cinnawa kanta wuta

Dabo Online
UA-131299779-2