Borno: Zulum yasa a binciko dalilin dake haddasa yawan masu kamuwa da cutar koda

Gwamnan Borno, Babagana Zulum ya bawa kwararrun masana umarnin a binciko dalilin dake haddasa yawan samun masu matsalar ciwon koda a fadin jihar Borno.

Majiyar Dabo FM ta bayyana cewa mai magana da yawun gwamnan jihar, Isa Gusau shine ya shaidawa majiyar mu da sanyin safiyar Alhamis.

Gusau yace “Gwamnatin jihar Borno ta aika da gayyatar kwararrun masana a fadin kasar nan domin su bincika abinda ke janyo cutar koda musamman a jihar Borno.”

“Masu binciken zasu maida hankali ne a fannin ruwan sha, mahalli da sauran ababen dake janyo gazawar koda.”

Gwamnan Borno dai ya sanar da fara yaki da cutar koda ne a lokacin daya kai ziyara asibitin kwararru na maiduguri bangaren wankin koda cikin karshen shekarar 2019, inda nan take ya sanar da yaki da cutar cikin gaggawa.

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.