Labarai

Kwabid-19: NARICT ta samar da sinadaran kashe kwayoyin cuta

A kokarin ta na taimakawa kokarin gwamnati domin yaki da cutar sarkewar numfashi ta Covid-19 da ta addabi sassan duniya, Cibiyan bincikan sinadarai ta kasa wato National Research Institute for Chemical Technology Zaria (NARICT) ta samar da sinadarin kawar da kwayoyin cuta musamman masu naso da wanda idanuwa basa iya ganin, har ma da mai bin iska.

Sinadaran wanda aka samar a bisa binciken kwararru da suke aiki da bangarorin kimiyya na Cibiyar, Yana da manufar amfanar da al’umma ne musamman a wuraren taruwan su.

Da yake zantawa da Dabo FM jim kadan bayan kammala kaddamar da sinadarin, shugaban Cibiyar Mista Joefry Birnimas Ya ce, duba da halin da Najeriya ta shiga musamman saboda barkewar cutar Covid-19, kuma aka samu karancin sinadaren kashe kwayoyin cutar musamman wanda al’umma za su rika amfani da su a yankunan su, ta sanya a matsayin su na kwararru akan harkar bincikr suka dukufa wurin lalubo hanyoyi samar da sinadarin ta hanyar amfani da itatuwa da suke cikin al’umma.

Kuma suna fatan samar da sinadaran ya kara daga darajar Najeriya a idanun kasashen duniya, domin a baya sai an fita kasashen ketare ake shigowa da irin wadannan kayayyakin.
Kuma ya bada tabbaci akan itatuwar da aka yi amfani da su wurin hada sinadaran.

Aikin samar da wadannan sinadaran, aiki ne na hadin gwiwa tsakanin kwararru musamman a fannin kimiyya da kuma suke aiki da Cibiyar, baya ga hadin gwiwa da aka samu daga wasu masana kiwon lafiya daga wasu wurare kamar Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, a cewar Mista Jeffry Barminas.

Sai dai babban abun da ke ciwa kwararrun tuwo a kwarya a cewar shi, shi ne matsalar kudi da zai taimakwa wurin kara inganta kayyakin da suka samar musamman domin amfanin mutanen karkara.
Sai ya bukaci shigowar gwamnatoci a kowwanne mataki domin ta haka ne za’a taimaki kokarin masana da karfafa masu gwiwa domin inganta kwazon su.

A jawaban su daban-daban, wasu daga cikin kwararrun da suka jagoranci samar da sinadarin, Mista Adelaye J Olatunji da Dakta Ochigbo Victor, sun bayyana yadda suka samu nasarar samar da sinadaran a matsayin wani babban cigaba da tarihin Narict ba zai taba mantawa da shi ba, kuma suka yi fatan shigowan gwamanti da masana da kuma sauran masu ruwa da tsaki domin ta haka ne za’a samu inganta bangaren bincike da kuma karfafwa sauran cibiyoyin binciken ma’adanai da sinadaran Najeriya.

Karin Labarai

UA-131299779-2