Sarkin Musulmi Saad III
Labarai

Yanzu-yanzu: Sarkin Musulmi ya dakatar da gabatar da Sallar Idi

Mai alfarma Sarki Musulmi, Abubakar Saad III ya bayar da umarnin dakatar da gudanar da Sallar Idin karamar Sallah cikin jami’i wajen gari, gaba ko kan iyakar garuruwan a fadin tarayyar Najeriya.

Sarkin Musulman ya bayar da umarnin ne cikin wata sanarwa da ya fitar mai dauke da sa hannun sakataren Jama’atul Nasril Islam, Dr Khalid Aliyu.

Sarkin Musulmin ya yi kira ga daukacin al’ummar Musulmin Najeriya da su gudanar da Sallar Idi a gidajensu cikin iyalai ko kuma mutum yayi ta shi kadai idan yana wajen da shi kadai yake rayuwa.

Kazalika ya yi kira ga dukkanin gwamnonin Najeriya da suka yanke shawarar gudanar da Sallar Idi da su tabbata sun kula da dukkanin shawarwarin da masana lafiya su ka gindaya musu.

Ya yi kira a garesu da su tabbata masu halarta sallar sun yi amfani da hanyoyin kariya kama daga wanke hannu da nesanta da juna tare da yin amfani da ‘Hand Sanitizer.

Cikin sanarwar, yace hukumomin zasu iya amfani da wasu masallatai dake kusa da su idan filayen da za ayi sallar sun cika bisa tsarin kiwon lafiya.

Karin Labarai

UA-131299779-2