Wata mata ta haihu mintuna 30 bayan gane tana dauke da juna biyu

dakikun karantawa
Hoton jaririn (2016)

Wata mata mai suna Ally Opfer mai shekara 26 ta haihu a cikin minti 30 da ta gane tana dauke da juna biyu.

Ta shiga fara lakuda duk kuwa da ta ce bata da masaniyar tana dauke da juna biyu a jikinta. Matar ta haihu mintuna 30 bayan ta gane tana dauke da juna biyu.

Ta ce ba ta da masaniyar abinda yake cikinta sakamakon gwaje-gwajen tabbatar da juna biyu suka tabbatar mata da ba ta dauke da komai a cikinta. Kazalika ta ce babu alamar dagowar ciki a jikinta.

Matar da ta ke a garin Cleveland na kasar Amurka ta ce ta yi ta shirin tafiya aikin da ta ke yi na baiwa ‘yan wasa kwarin gwiwa yayin harkokin wasanni, sai dai ta ce ta rika jin wani sauyin yanayi a jikinta, wanda duk da hakan ba ta kawo tana dauke da juna biyun ba, kamar yadda Jaridar The Sun Burtaniya ta rawaito.

Kamar yadda jaridar ta rawaito, matar ta ce; “Ban yi tsammanin ina dauke da juna biyu ba. Eh lallai yanayin al’adata ya canza, amma daman ya saba yi min haka. Ban yi kiba ba, bana jin gajiya ko jin motsi a ciki na.”

“Ciki na bai daga ba yana kwance. Don haka babu wata hanya da zan ce ina dauke da juna biyu. Duk da haka saboda ciwo ya kan zo min ya tafiya, na je gwajin juna biyu domin na tabbatarwa kai na. An tabbatarmin bana dauke da shi.”

Bayan wasu awanni, ta ce ciwon ya yi tsanani sosai, an kai ta asibiti tana ihun ciwo bayan da ta bar iyayenta su kai ta ganin likita.

Ta ce likitan ya ce akwai wani abu a cikinta mai nauyi. Ta tambayi likitan ko cutar daji ce, ya ce mata aa.

Ta kara da cewa; “Ina gama magana na amsa masa da a’a, ya ce miki ina dauke da juna biyu na tsawon makonni 38. Kina cikin nakuda ne a yanzu. Ya kamata mu shiga da ke dakin karbar haihuwa, haihuwa za ki yi.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog