Custom zata kashe Biliyan 3.1 kudin share-share, 128m na kallon ‘Tv’, 78m na ‘Photocopy’

Majalisar dattijai ta Najeriya ta rattaba hannun kan kasafin kudin hukumar hana fasa kauri ta kasa wanda za’a kashe jimlar kudi har naira biliyan 238 cikin shekarar 2020.

Majiyar Dabo FM ta ruwaito cewa majalisar ta zartar da kasafin kudin ne bayan shugaban kwamitin kasafin kudin hukumar hana fasa kauri ta kasa na majalisar, Francis Alimikhena ya gabatar domin yin nazari.

Cikin kasafin kudin hukumar dai an ware Biliyan 98 cikin Biliyan 238 a kan hakkokin ma’aikatan hukumar, Biliyan 15 na rara saboda abinda kaje ya dawo, Biliyan 123 na gundarin manyan aiyuka.

Bayan haka an ware miliyan 128 na talabijin da kayan kallo, miliyan 30 kudin tebur da kujeru, kudin kayan share-share, sikana, dana hasken lantarki an ware Biliyan N3.1 ; Miliyan N21.7 da kuma miliyan N927.

Masu Alaƙa  Duk wanda ya shigo da kaya na sama da N50,000 Najeriya, zai biya haraji - Kwastam

Miliyan 63 kudin firji, Miliyan 173.7 kudin agogon bango da kayayyakin fayal fayal, samar da ruwa zai lamushe Miliyan 577, na’urorin ‘Photocopy’ Miliyan 74, za’a aje Biliyan 15 a gefe, Miliyan 20 kudin dinki, Miliyan 70 na hawa yanar gizo, Milyan 20 ta jaridu da littafai.

‘Yan majalisa sun bayyana ra’ayoyin su kafin zartar da kudin, wasu sunce komai yayi dai dai, sai dai dan majalisa mai wakiltar Kebbi ta kudu, Sanata Bala Na’Allah ya bayyana rashin amincewa da wasu abubuwa daga kasafin kudin hukumar.

Na’Allah yace “meya samu tsoffin kayan kallon da suke dasu, shin kallo kawai zasu je su shantake sunayi a wajen aiki.”

Masu Alaƙa  Duk wanda ya shigo da kaya na sama da N50,000 Najeriya, zai biya haraji - Kwastam

Daga karshe dai majalisar dattijai ta aminta da kafatanin kasafin kudin hukumar ta kwastam, inda kuma ta zartar nan take. Kamar yadda TheCable ta fitar.

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.