0
Muhammad Aliyu
Jami’in rundunar yan sandan Najeriya, Eze, ya rataye kanshi a bayan kantar sashin binciken manyan laifuka dake Yaba.
An dai garkame dan sandan ne bayan zargi da ake akanshi na harbe wani mutum ba bisa ka’ida ba.
“An kawoshi cibiyar ne domin a bincike shi tare da hukunta shi.”
“Da misalin karfe 2 na dare, ya rataye kanshi.”, kamar yadda majiyar PUNCH ta tabbatar.
A nata bangaren, rundunar yan sandan jihar ta hannun kakakinta, Bala Elkana yace a dakance shi zai yi bayani daga baya.
