Tallafin Kwabid-19: Jigawa ta karbi tirela 110 na kayan abinci daga gwamnatin tarayya

Karatun minti 1
Tallafin Kwabid-19

Tallafin Kwabid-19: Gwamnatin Jihar Jigawa ta karbi kayan abinci tirela 110 daga cikin tireloli 150 da gwamnatin tarayya ta bayar gudummawa domin rage radadin Koronabairas.

Gwamnan jihar, Muhammadu Badaru Abubakar ne ya bayyana haka a yayin wata ganawa da yayi da manema labarai a fadar gwamnatin jihar dake garin Dutse.

DABO FM ta tattara cewar gwamna ya shaida cewar; tini gwamnatin ta aike da kayayyakin abincin zuwa akwatunan zabe inda a cewarsa kowanne akwatin zabe zai samu tan daya da za a raba wa mutane a kalla 100.

Gwamnan ya kara cewa a kalla mutane 350,000 ne za su amfana daga tallafin rage radadin da gwamnatin tarayya ta aikewa jihar.

DABO FM ta tattara cewar shugaba Muhammadu Buhari ya alkauranta baiwa ‘yan Najeriya kayayyakin tallafi domin rage radadin cutar Kwabid-19 a wani jawabinsa da ya gabatar a rana 29 ga watan Maris.

 

Gwamna Badaru ya ce baya ga tallafin gwamnatin tarayya, kungiyar manyan yan kasuwar jihar za su bayar da nasu tallafin na kayan abinci.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog