Da ‘Dumi ‘Dumi: Boko Haram sun kai hari Chibok

‘Yan ta’addan kungiyar Boko Haram sun can suna kone gidajen al’umma a kauyen Mifa da ke karamar hukumar Chibok na jihar Borno.

Wani mazaunin kauyen ya shaidawa The Cable cewa ‘yan ta’addan sun shigo kauyen misalin karfe 8 na dare kuma nan take suka fara bankawa gidajen al’umma wuta.

“Suna kone gidaje a halin yanzu da muke magana da kai, sun zo da yawa a kan babura sun fara kone-kone,” a rahoton TheCable.

“Sun kone gidaje da yawa.”

Masu Alaƙa  N3000 ce tayi sanadiyyar shigarmu Boko Haram - Tsohon dan Boko Haram

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.