Labarai

Da Dumi Dumi: Dana ya kamu da cutar Coronavirus – Atiku Abubakar

Tsohon mataimakin shugaban kuma dan takarar shugaban in kasa a karkashin jam’iyyar PDP cikin shekarar 2019, Atiku Abubakar ya tabbatar da cewa dansa ya kamu da cutar Coronavirus.

Majiyar Dabo FM daga jaridar TheCable ta bayyana Atiku ya bayyana hakan me a shafin sa na Twitter, inda ya bayyana cewa dan nasa ya kamu da cutar a ranar Lahadi.

Ya kuma tabbatar da cewa hukumar ‘Nigeria Centre for Disease Control (NCDC)’ ce ta tabbatar da haka, inda yanzu haka ya bayyana an mayar dashi babban asibitin Gwagwalada dake babban birnin tarayya dake Abuja.

Karin Labarai

UA-131299779-2